Fafatawa da za’a yi tsakanin Poland da Argentina za ta kasance karon-battar kungiyoyin biyu ne, ba ‘yan wasan gaba Robert Lewandowski da Lionel Messi ba, in ji Kocin Poland Czeslaw Michniewicz.
Kocin na Poland ya bayyana hakan ne jiya Talata kafin wasansu na karshe a rukunin C na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.
Poland ce ke jagorantar rukunin, kuma kunnen doki ya isheta ta kai zagayen ‘yan 16.
Sai dai bayan da ta yi rashin nasara na ba-zata a hannun Saudiyya a wasansu na farko, nasara a wannan wasa ne kadai za ta ba Argentina damar zuwa matakin gaba a gasar.
Yin kunanen doki zai iya sa Argentina ta shiga zagaye na gaba, amma ya danganta da yadda sakamakon daya wasan rukunin zai kaya.
Messi da Lewandoki ba su taba yin wasa da juna a matakin kasa da kasa ba, amma sau uku suna haduwa a gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League.
Argentina dai ta lashe wasanni shida cikin 11 da bangarorin biyu suka taba bugawa, inda Poland ce ta lashe wasa na karshe da suka hadu a 2011