Karawar Najeriya Da Masar A Gasar AFCON

Ahmed Musa, hagu da Mohamed Salah, dama (Hotuna AP)

Lokaci na baya-bayan da suka kara a shi ne a wasan sada zumunci da aka yi a birnin Asaba a 2019 inda Super Eagles ta doke ‘yan wasan Pharaohs da ci 1-0.

A yau Talata Najeriya za ta kara da kasar Masar yayin da gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON ta shiga rana ta uku.

Kamaru ce mai karbar bakuncin wannan gasa.

Manyan kasashen za su kara ne a rukunin D a filin wasa na Roumde Adija da ke garin Garoua.

Sau bakwai Masar na daga kofin yayin da Najeriya ta lashe sau uku.

Lura da muhimmancin samun nasara wasan farko, bayanai na nuni da cewa dukkan bangarorin biyu sun shirya tsaf.

Wasu da dama na ganin Najeriya za ta fuskanci kalubale yayin da ta tunkari gasar da kocin wucin gadi Augustine Eguavoen da ya canji Gernot Rohr.

Sai dai wasu na ganin irin kwarewa da gogewa da Super Eagles suka yi na zuwa gasar akai-akai, zai ba su damar shawo kan duk wani kalubale da ake masu hange.

A gefe guda kuma, ‘yan wasan Pharaohs na Masar karkashin mai horarwa Carlos Queiroz sun kimtsa tsaf lura da cewa tawgarsu na dauke da daya daga cikin shahararrun ‘yan wasan kwallon kafar duniya – Mohamed Salah.

Bayanai sun yi nuni da cewa kasar ta Masar a wannan karon ba za ta zama kanwar lasa ba yayin da ta kuduri aniyar daukan kofin a karo na takwas.

Tun daga 1960, sau 18 Najeriya da Masar ke karawa a gasar ta AFCON, inda Najeriya ta yi nasara lashe wasa takwas yayin da Masar ta lashe biyar, sauran kuma aka yi kunnen doki.

Lokaci na baya-bayan da suka kara a shi ne wasan sada zumunci da aka yi a birnin Asaba a 2019 inda Super Eagles ta doke ‘yan wasan Pharaohs da ci 1-0.