ZABEN2015: Karar Hana Amfani da Na'urar Tantance Katin Zabe ta Samu Cikas

Tambarin Hukumar Zaben Najeriya.

Yayin da zaben Najeriya ke ci gaba da karatowa ana kai ruwa rana game da yin amfani da na'urar tantance katin zabe.

Bukatar da wasu jam’iyun siyasa hudu suka gabatar a gaban kotu na hana yin amfani da na’urar tantance katin zabe ta samu cikas.

Jam’iyun da suka hada da UDP da AA da ACPN da kuma AD suna nuni da cewa sashi na 52 na dokar zabe bai amince a yi amfani da na’ura ba, saboda haka a dakatar da kokarin yin amfni da na’urar tun gabanin kammala shari’ar.

Sai dai alkalin babbar kotun tarayya da ke sauraren karar, Adeniyi Ademola, a Abuja ya ki amincewa da wannan bukata, inda ya nemi hukumar zabe da ta zo ta kare kanta a ranar 10 ga wannan wata na Maris.

Your browser doesn’t support HTML5

NA'URAR ZABE