Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kalabalge dake Jihar Borno Babagana Malarima ya jagoranci wata tawaga daga karamar Hukumar zuwa Abuja inda suka kawo kokon baransu zuwa wajen 'ya'yansu da ke majalisar kasa.
A wata hira da manema labarai bayan isarsu Abuja, Alhaji Malarima ya bayyana cewa mutanen al'ummaru sama da dubu 40 suna bukatan taimako na gaggawa saboda bisa ga cewarshi, abincin da mutanen da suke da shi gaba daya, Boko Haram sun hana su tabawa sun kore su baki daya daga garin. Yace zuwa gaba kadan, idan damina ta sauko, jama’a zasu shiga cikin yunuwa da matsala sosai saboda karancin abinci.
Kalabarge na daya daga cikin kananan hukumomin da kungiyar Boko Haram ta daidaita a jihar Borno, inda a halin yanzu dunbin al’ummar ke fakewa a dazuka dake kan iyaka tsakanin Borno da kasar Kamaru.
Ga cikakken rahoton da wakiliyarmu Sashen Hausa Madina Dauda ta aiko mana.
Your browser doesn’t support HTML5