‘Yan sanda sun mikawa karamar hukumar ajiyar shanun ne bayan sun kwato su daga hannun barayi. Hukumomin karamar hukumar sun bayyana cewa, lalurar rashin lafiya ne yasa suka kai shannun kasuwa.
A cikin hira da Muryar Amurka shugaban kungiyar miyatti Allah na jihar Naija Hardo Adamu Kaduna yace kimanin shanu dari ne aka sace masu a jihar Naija, kuma kawo yanzu ko guda daya ba a mayar masu ba. Bisa ga cewarsa, hukumomin karamar hukumar sun shaida masu sun sayar da wadansu shannun yayinda suka tura keyarsu zuwa asibitin dabbobi inda suka ce ana yiwa sauran shannun jinya.
Wadansu makiyayan da Sashen Hausa ya yi hira dasu sun ce sun ga shanunsu a kasuwa inda aka kai domin saidawa, yayinda suka kuma bayyana cewa, ba a basu koda anini ba na kudin da aka ce an sayar da sauran shanun.
Da yake maida martini, Alhaji Garba Yarima mataimakin shugaban karamar hukumar Bosso, kuma shugaban kwamitin kula da shanun ya tabbatar da kai shanu uku kasuwa da yace basu da lafiya, da nufin sayar da su ayi jinyar sauran da yace basu da lafiya. Sai dai bai bayyana adadin shanun da aka basu ajiya ba.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya aiko daga Minna, Jihar Naija Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5