Shugabannin Fulani yanzu haka sun saka ido kan kasuwar dabbobi dake Abuja, saboda barayin shanu daga yankin arewa maso yammacin kasar, sun maida kasuwar Dede babbar hanyar batar da dabbobin da suka sato.
Da yake karin bayani kan haka, shugaban Fulani na yankin Abujan, Ummaru Dan Deli, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya cewa, sun gano shanu 18 da aka sato daga jihar Zamfara.
Dan Deli yace, ko wanda ba baFulatani ba, da ganin wadannan dabbobi yasan cewa na sata ne. Saboda wasu shanun suna da ciki, kuma babu baFulatani wanda cikin hankalinsa da zai sayar da shanunsa alhali suna da ciki.
Tuni shugabannin Fulanin suka mika wanda ake tuhuma da kawo shanun kasuwa ga jami'an tsaro a ofishin 'Yansanda da suke Zuba, wadanda suke gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hanu a sace sacen dabbobin.
Maitaimakawa jami'an tsaro gano barayi, Alhaji Ali Kora, yace abun da ban takaici, domin akwai hanun wasu ma'aikatan hukuma a batar da shanun sata.
Ga karin bayani.