Kamfanin mai na kasa NNPC ya kara farashin mai a famfo zuwa N855 da N897 a kowace lita daga N617/l kwanaki kadan bayan kamfanin man na kasa ya amsa cewa yana fama da matsalolin kudi. 'Yan kasuwa masu zaman kansu sun kara farashin su tsakanin N930 zuwa N1,200/l.
A kasar da farashin man fetur yake mummunan tasiri a kan farashi kayayyaki, musamman sufuri, abinci, da sauran muhimman abubuwan rayuwa, wannan wani lokaci ne mai tattare da damuwa. Masu sana'ar sufuri a manyan biranen kasar sun kara farashin da ya kai kashi 50 cikin 100. Masu daukar motar haya yanzu suna tafiya mai nisa zuwa aiki ko kuma ba sa fitowa kwata-kwata. Masu kasuwanci suna jin tsoron rashin ciniki.
’Yan Najeriya ba su da numfasawa daga hauhawar farashin kayayyaki da ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa da ta shafi dukkan kayayyaki da ayyuka tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya soke tallafin man fetur a watan Mayun 2023. Farashin ya tashi daga N195 zuwa sama da N600 sakamakon faduwar darajar Naira.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya hakikance cewa kamfanin na NNPC na iya durkushewa idan ya ci gaba da ba da tallafin man fetur. ‘Yan Najeriya sun ji takaicin yadda tashin farashin ya zo daidai da sanarwar cewa matatar man Dangote ta fara aiki amma ba tare da samun rage farashin mai kamar yanda aka yi hasashen ba.
Fatan samun saukin tsadar rayuwa a Najeriya da aka fara gani yanzu ya fuskanci cikas. Habakar hauhawar farashin kayayyaki ya ragu kadan a cikin watan Agusta zuwa kashi 33.4 cikin dari, daga kashi 34.19 cikin dari a wata daya baya. Sabon tashin farashin mai na baya-bayan nan na kashi 66.4 cikin dari zai dawo da tsadar kayayyaki.
Wannan abu dake faruwa ya kawo cikas hasashen babban bankin CBN na samun raguwar tsadar rayuwa ta dawo zuwa kashi 21.4 cikin 100, wanda Gwamna Yemi Cardoso, ya yi fata a watan Fabrairu, wanda ya ce za a cimma ta hanyar manufofin bankin na dakile hauhawar farashin kayayyaki.
Ma’aunin tsadar rayuwa ya tashi daga kashi 22.4 cikin dari zuwa kashi 33.95 cikin dari a watan Mayun 2023, shekara guda bayan cire tallafin man fetur da faduwar darajar Naira. Wannan shine alkaluma mafi girman tun watan Maris shekarar 1996, bugu da karin watanni 16 a jere ana samun karuwar farashi. Bankin zai zurfafa binciken dabaru don magance wannan yanayin da ke faruwa.
Akwai hadarin sake fuskantar zanga-zangar kungiyoyin kwadago, dalibai da kungiyoyin farar hula don kalubalantar karin farashin man fetur, lamarin dake nufin dole ne gwamnati ta shiga cikin tattaunawa mai ma’ana tare da duk masu ruwa da tsaki.
Dole ne gwamnati ta tabbatar da cewa an daidaita farashin man fetur a cikin gajeren lokaci tare da samar da wadataccen mai daga matatun gida. Kuma wajibi ne a kara duk wata matatar mai ta cikin gida a shirin sayar da danyen mai na naira da ake yiwa matatar Dangote. Ya kamata a sayar da matatun mai na NNPC kai tsaye. Idan aka yi la’akari da tarihinsu mai cike da rudani, babu wani mai saka jari da ya san abin da yake ciki da zai kulla wata yarjejeniyar aiki da su kamar yanda aka shawarta.
-Punch-