Ko da yake a shekarar 1991 aka fara tunanin kebe rana ta musamman domin matasan duniya, amma a shekarar 1998 ne Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ware ranar 12 ga watan Agusta na kowace shekara ta zamo ranar gangami da fadakarwa domin ankarar da al’umar duniya, musamman hukumomi da gwamnatoci, dangane da muhimmancin kula da rayuwar matasa da kuma kiyaye hakkokin su ta yadda za su amfani al’umma.
Taken ranar na ta bana shine "kirkiro da sabbin dabarun sana’o’i da kirkire-kirkire masu alfanu ga matasa domin ci gaba mai dorewa," kuma wasu daga cikin matasan Najeriya sun tofa albarkacin bakin su.
Wani matashi mai suna Nuhu Mohammed Hassan na cewa, “Gaskiya galibin matasa ba su san ma mecece ranar matasan ba, amma abin da zan iya cewa, don Allah matasa su rinka amfani da wannan rana wajen aika sakonni ga shugabanni da ‘yan uwa na fadakarwa domin zaman lafiya da kuma yadda ci gaba zai zo musu.”
Shi kuwa Aliyu Mohammed Shettima cewa yake, “Gaskiya idan zan baiwa matasa shawara zan ce su baiwa sana’ar hannu muhimmanci, saboda wadannan shugabannin namu ba son ci gaban mu suke ba, koma suna yi ne domin masalahar kan su kowa ya nemawa kan sa mafita.”
Comrade Abubakar Mohammed Janar, shine tsohon mataimakin shugaban majalisar matasa ta Najeriya, ya yi tsokacin dangane da taken ranar matasan na bana. “Idan aka yi la’akari da wannan take, za’a iya cewa Majalisar Dinkin Duniya kamar Najeriya suka kalla suka sanya wannan take, domin kusan mun fi kowa ci baya ta wannan fuskaka. Kashi 70% (na 'yan Najeriya) matasa ne ‘yan kasa da shekaru 27 kuma galibin suna fama da rashin sana’a ko aikin yi.”
To sai dai Malam Abdullahi Dauda wanda ke da cibiyar buga takardu da zane-zanen fasahar sadarwa da komfuta, duk da cewa yana da sana’ar yi tun shekaru 10 da suka gabata, ya fayyace kalubalen da masu sana’o’in hannu ke fuskanta.
Ya ce “rashin tallafi domin fadadawa ko bunkasa sana’o’in mu shi ne babban kalubalen mu, akwai bukatar hobbasa daga gwamnati domin mu rinka koyawa yaran mu, su koya kuma suna bude nasu guraren sana’oin.”
Hakan dai na nuna tsananin bukatar da ke akwai ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya su kara kaimi wajen tsare-tsaren da suka ce suna fito dasu domin tallafawa matasa su tsaya da kafafun su.
Saurari shirin a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5