Da almurun Talatar nan ce jirgin ya kife dauke da fasinjoji, wadanda galibin su daliban makarantar Islamiyya ne.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da wannan mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.
A sakon da ya aike wa gwamnati da al’ummar jihar Kano na jajanta musu kan wannan mummunan lamari, shugaban ya tabbatar wa gwamnatin jihar goyon bayan dukkanin hukumomin tarayya a jihar, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Yanzu haka dai gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai binciko musabbabin wannan hadari karkashin jagorancin kwamandan sabuwar cibiyar kula da lamuran sojojin ruwa da aka kafa a nan Kano a bana, Navy Captain Muhammad Abubakar Alhassan.
Hakazalika gwamnatin ta Kano ta amince a fitar da naira miliyan 6 domin bada tallafin abinci ga iyalan wadanda suka rasa yaya da yan uwa da kuma maguguna ga wadanda suka jikkata.
A shekara ta 2008 ma makamancin wannan hadarin kwale-kwale ya wakana a madatsar ruwan ta Bagwai, wanda ya kashe mutane kimanin talatin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5