Kungiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars (Sai masu gida) dake tarrayar Najeriya, ta cigaba da rike matsayinta na wasanni biyar a Jere ba tare da an samu nasara akanta ba inda a jiya kungiyar ta yi tattaki har Akure suka yi canjaras 0-0 tsakanita da kungiyar Sunshine a wasan mako na takwas a Firimiya lig na tarayyar Najeriya na bana.
Da yake jawabi ga manema labarai, bayan tashi a wasan, Kocin kungiyar Kano Pillars Ibrahim A Musa, ya yaba wa ‘yan wasan bisa namijin kokarin da suka yi wajan kare martabar kungiyar da ma Jihar Kano a fagen wasan kwallon Kafa.
Bayan haka Kocin ya gode wa gwamnatin jihar Kano Karkashin Gwamna Umar Abdullahi Ganduje, na jihar bisa kokarinsa na taimakawa kungiyar wajen biyansu hakkokinsu da kuma kyautata wa gami da kulawa dasu a duk inda suke wasa walau a gida ko a waje.
Haka kuma mai horas da ‘yan wasn Ibrahim A Musa, ya ce shima alkalin wasan da ya hura wasan mai suna Damian Akure, daga jihar Benue ya cancanci yabo bisa yanda yanuna kwarewar sa a wasan ba tare da wata matsala ba.
Kano Pillars ta buga wasannin ne kamar haka:
Ranar 24/1/2018
Kano Pillars 2
Abia Warriors 0
Ranar 28/1/2018
El-kanemi Warrios 0
Kano Pillars 0
Ranar 31/1/2018
Kano Pillars 2
Plateau United 0
Ranar 4/2/2018
Kano Pillars 2
MFM Fc 0
Ranar 11/2/2018
Sunshine Stars 0
Kano Pillars 0
Kamar yadda Jami'in watsa labarai na kungiyar Malikawa ya shaida mana,
Kungiyar ta Kano Pillars da tana mataki na uku ne a saman teburin Firimiya lig da maki 15 a wasanin Mako na takwas.
A Ranar lahadi mai zuwa 18/2/2018 kungiyar Kano Pillars (sai masu gida) zasu karbi bakuncin Enyimba, a wasan mako na 9 a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata Kano.
Your browser doesn’t support HTML5