Aikin da aka rabbata hannu tsakanin gwamnati da kamfanin da zai gina gadar na daga matakan gwamnati na saukaka zirga zirgar Jama’a, musamman wadanda ke ziyartar birnin na Kano daga jihohi arewa maso gabashin Najeriya.
Kwamishinan ayyuka na jihar Kano Idris Garba Unguwar Rimi, ya rattaba hannu akan daftarin kwangilar gina gadar.
Masu ababen hawa dake shiga Kano daga Jihohin arewa maso gabashin Najeriya guda da-ma wasu bangarori na kasar da kuma sassan Jamhuriyar Kamaru da Chadi na amfani da wannan sashi ne wajen shiga birnin Kano domin hada hadar kasuwanci, sha’anin zamantakewa da mu’alar yau da kullum.
Karin bayani akan: NNPC, jihar Kano, Nigeria, da Najeriya.
Kazalika, wasu na shiga birnin Kanon ta wannan sashi domin wucewa Jihohin dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ko kuma kasashe makwafta irin su Jamhuriyar Nijar, Benin, Mali da sauran su.
Gadar wadda za’a gina akan shatale-talen gidan mai na NNPC, kamfanin TRIACTA ne zai gudanar da aikin akan tsabar kudi kusan naira biliyan tara, kamar yadda kwamishinan ayyukan na Kano Idris Garba Unguwar Rimi.
Hakan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan kalaman kushewa da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso yayi game da aikace aikacen da gwamnatin Kano ke yi, inda yace al’umar Kano Ilimi suke bukata, amma ba gine ginen gadoji ba.
Saurare cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5