WASHINGTON, D.C —
Asalin mazuna garin Gamdu mafarauta ne da suka fito daga Gamdu ta arewacin Maduguri a jihar Borno, zuwa Kano.
Dattijon Garin, Malam Musa Gamdu mai kimanin shekaru 80, ya ce asalin kakanninsu barebari ne mutanen Kukawa, arewa da Maiduguri. Ya kuma ce sama da shekaru 20 kenan da kafa garin na jihar Kano.
Dattijo Musa ya ce suna da bukatar ruwa da wutar lantarki kuma suna bukatar gwamnati ta dama da su a harkokinta.
Saurari cikakken shirin wanda Adamu Ibrahim Dawakin Tofa ya gabatar.