Kanfanin Uber Ya Dakatar Da Shirin Kera Motar Jigilar Kaya Mai Tuka Kanta

Katafaren kamfanin jigilar fasinja Uber, ya bayyana dakatar da ci gaba da inganta dabarun kera babbar mota mai tuka kanta da ya dauki lokaci yana gudanar da bincike kan yadda zai fara amfani da ita, a maimakon haka zai mayar da hankali wajan inganta karamar mota mai tuka kanta ta jigilar fasinja.

A ranar litini data gabata ne kamfanin ya bayyana kudirin san a ci gaba da inganta kananan motocin jigilar fasinja masu sarrafa kansu wadanda kamfani ya dade yana kokarin ganin ya tabbatar da fara amfani da su.

Kamfanin yayi kokarin kera manyan motocin jigilar kaya domin rage matsalar jigilar kayan nauyi zuwa wurare masu nisa musamman ganin yadda direbobin manyan motoci ke barje gumi musamman a lokacin doguwar tafiya.

Sai dai kanfanin ya bayyana cewa lamarin ba zai shafi bangaren Uber Freight ba, shi dai wannan bangare an kaddamar da shi ne a watan 7 na shekarar 2017, domin saukakawa direbobin manyan motoci masu jigilar kaya samun damar sanin inda zasu sauke ko daukar kaya da nisan inda zasu kai kayan, da kuma adadin kudin da zasu iya samu.

Ana iya samun Uber Freight, wanda a ya fara aiki a yankuna uku na kasar Amurka, da daukacin nahiyar kuma yana ci gaba da aiki, kuma wannan jari da kamfaninj ya zuba, kawo yanzu ya nunka har zuwa sau uku daga lokacin da ya fara aiki.