WASHINGTON D.C —
Hoton wata matashiya ‘yar asalin Najeriya mai shekaru biyar da haihuwa ya yi matukar daukar hankalin jama’a a shafukan yanar gizo musamman ganin yadda kowa ke tofa albarkacin baki da kalamai irin su; abin mamaki, kyakkyawa, tubarkalla, da sauran su.
Shafin yahoo ya wallafa cewa a ranar juma’a data gabata ne shafin Instagram na wata mai daukar hoto Mofe Bamuyiwa, ta wallafa hoton wata yarinya mai suna Jare, inda ta rubuta “babu shakka mutum ce” wannan mai daukar hoto ta zama a jihar Legas dake Najeriya.
Ana kyautata zaton sama da mutane dubu 20, ne suka kalli wannan hoto tare da tofa albarkacin bakin su akan irin kyau da wannan yarinya ta yi.
Mun samo labarin ne daga shafin yahoo.
Facebook Forum