Kananan Hukumomi na Mazauna Karkara ne

Shugaban ma'aikatan kananan hukumomin Najeriya Ibrahim Khalil yace baiwa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu ne zai taimaka wajen kyautata rayuwar karkara.

Yace anyi watsi da tsarin kananan hukumomi, wanda hakan ke jawo biyan albashi ma ya yi wuya a wasu wuraren. Yace duk jihar da mutum ya je zai ga kananan ma'aikata an dorasu kan manya. Yace wannan almundahana ce mafi girma wadda ya kamata EFCC ta dinga kalla ba lallai maganar kudi ba kawai. Misali mutumin da aka daukeshi a bangaren aikin noma sai a turashi wurin kasafin kudi.

Ibrahim Khalil ya kara da cewa suna neman tsare-tsaren da zasu tabbatar da 'yancin kananan hukumomi da hana gwamnoni yi masu karan tsaye a harkokinsu. Gwagwarmayar da suke yi da fadawa duniya ta gidajen rediyoyin kasashen waje suka sa yanzu mutane sun fara ganewa. Yace ba'a bar masu kananan hukumomi su yi abun da suke so ba. Mutanen da suke karkara, talakawa da wadanda ake ganin su ba komi ba ne su ne da kananan hukumomi.

Manoma, masaka da masu kananan sana'o'i an yi kananan hukumomi ne dominsu. Ba'a yiwa gwamnoni ba. Idan an inganta kananan hukumomi babu dalilin da zai sa mutane suna barinsu zuwa manyan birane.

Inda ba'a manta ba shugaba Muhammadu Buhari a jawabinsa yayi alkawarin sa ido akan kananan hukumomi gani cewa ba ayi sama dafadi da kudadensu ba.