ABUJA, NIGERIA - Rahoton ya gano cewa kamfanonin mai da iskar gas guda 51 ne ke bin gwamnatin tarayya bashin sama da dala biliyan uku a shekarar 2020, batun da ya aza ayar tambaya kan an karkatar da kudaden ne daga asusun gwamnati.
Rahoton na hukumar ta NEITI na shekarar 2020 ya bayyana cewa Najeriya ta samu dala biliyan 20.43 daga bangaren mai da iskar gas a shekarar, adadin da ya nuna an samu raguwar kashi 40% idan aka kwatanta da dala biliyan 34.22 da aka samu daga fannin a shekarar 2019.
Malam Sa’ad Balarabe shi ne mataimakin darakta a hukumar kula da kudaden shigar da ake samu a man fetur da iskar gas da kuma ma’adinai a Najeriya NEITI ya yi wannan bayanin.
Rahoton ya kuma kara da cewa, yawan kamfanonin da suka kasa biyan bashin ya ragu daga 77 wadanda hukumar ta ruwaito a shekarar 2019 zuwa 51 a shekarar 2020.
Kamfanin kula da albarkatun man fetur na Najeriyar NNPC da ke da kyakyawan alaka da hukumar ta Neiti ta bakin babban jami’in kula da harkokin kudade na kamfanin Malam Umar Ajiya ya bayyana cewa sun himmatu wajen samar da bayanai ga al’umma da kuma inganta ayyukansu a kasar.
Wannan dai shi ne karo na 13 da hukumar NEITI tare da hadin gwiwar hukumar EITI ke fitar da irin wannan rahoto, kuma ya zuwa yanzu rahoton ya binciko biyan kuɗade haraji daga hukumomi guda tamanin da uku wadanda suka hada da kamfanonin mai da iskar gas guda sittin da tara da hukumomin gwamnati goma sha uku da kuma kamfanin iskar gas na Najeriya wato NLNG a takaice.
Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5