A wani yunkuri na kwantarwa da mutane hankali kan sakonnin da suke aikawa ta hanyar sadarwar nan mai farin jini, Kamfanin WhatsApp yace ya kare duk sakonnin da masu amfani da kafarsa ke aikawa.
Cikin wani sako da aka kafe kan internet shugaban kamfanin WhatsApp Jan Koum, yace duk wani sako da aka kafe zai sami tsaro daga lokacin da aka tura sakon zuwa lokacin da wanda aka aikawa ya sami sakon, wannan sabon tsari zai tabbatar da cewa mutumin da aka aikawa da sakon shine kadai zai iya karantawa.
Kamar yadda yace a rubuce, “babu wanda zai iya karanta sakon Ko da masu kutsen satar bayanai ne ko kuma gwamnati mai shiga zarafin mutane, ko su kansu kamfanin ba zasu iya ganin sakon ba.”
Wannan kokari da WhatsApp keyi don kare bayanan mutane ya zo ne alokacin da ake takaddama kan kare bayanai da sirrin mutane, kamar yadda kasar Amurka ta afka cikin muhawara kan tsaron kasa da kare ‘yancin sirrin mutane.
A cewar WhatsApp, wannan sabon tsaro zai zamanto kamar kofa ce da dan mukullinta. Mutanen da zasu iya shiga kadai sune masu dan mukulli a hannunsu, sun kuma kara da cewa duk lokacin da aka aika da wani sako zai zamanto a kulle yake da kuma dan mukullinsa, wanda ko kamfanin WhatsApp ba zai iya ganin sakon ba.
A cewar shugaban kamfanin Koum, sama da mutane miliyan daya ne ke amfani da wannan hanyar sadarwar, kuma Cikin shekara ta 2011 kamfanin Facebook ya sayi WhatsApp kan kudi dala Biliyan 19.