Kamfanin Wayar Hannu Na China Zai Fitar Da Babbar Waya

China tayi fice a kasashe masu tasowa wajen kera kananan wayoyi da kayan fasaha da mutane dayawa ke amfani da su.

Yanzu haka dai fitatcen kamfanin kera kayan fasahar nan mai suna Huawei, zai kaddamar da wata babbar wayar salula wadda masana ke ganin zata iya shiga layin sunayen manyan wayoyin da ake da su yanzu a duniya.

Huawei babban kamafani ne da tsohon sojan kasar China Ren Zhengfei ya kafa wanda ke kera kayayyakin fasaha musammam wanda suka shafi na sadarwa. Huawei na kera duk kayayyakinsa da yake amfani dasu a wayoyoyin da yake kerawa.

A cewar Clement Teo, wani masani kuma mai bincike kan kayan fasaha yace, kafin mutane su shaku da sabbin manyan wayoyin Huawei, dole ne sai ya dauki lokaci kuma kamfanin ya fitar da jerin manyan wayoyin da zasu sayar da kansu.

A shekarar da ta gabata dai kaso uku na wayoyin da aka sayar Miliyan 108, sun kasance manyan wayoyi ne da farashinsu ya wuce $300.

Sai dai masana na ganin tabbas kamafanin Huawei yana da sauran tafiya kafin manyan wayoyinsa su sami karbuwa a duniya baki daya.