Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Sunfi Bada Gudunmawa Mai Yawa Wajen Ciyadda Kasa Gaba


Dr. Ibrahim Gwarzo, ya cigaba da bayyana banabnce banbance da ake da su a tsakanin karatun kasar Amurka da gida najeriya, yace a kasar Amurka za aga ba haka su keyi ba, a nan Amurka sunfi bada mahimmanci a wajen daliban su fahimci abinda ake koya musu. Suna dagewa sosai su tabbatar da dalibai sun fahimci karatu dai-dai gwargwadon kwakwalwarsu. Lokacin jarrabawa ba za'a tambayi dalibi ya mai maita abunda aka koya mashi ba, sai dai yayi bayanin fahimtar shi daban da wadda a ka koya mashi.

Hasali ma, idan mutum ya maimaita yadda aka fada a littafi zai iya faduwa jarrabawar, domin anfi so aji tashi fahimtar. Abu na biyu shine bambancin karatun Najeriya da na kasar Amurka, shine wajen aiki da kimiyya da fasaha wajen koyarwa. malamai a nan Jami'ar ta Texas A&M da kuma sauran Jamio'i a nan kasar Amurka, suna matukar amfani da yanar gizo wato “internet” domin koyarwa da yada ilimi. Dalibi zai iya zaunawa daga gida ya saurari lacca daga bakin Malamai, zai iya yin tambaya kuma a amsa mashi duk ta cikin yanar gizo.

Dr Ibrahim yace karatun likita yana da matukar ban sha'war gaske. A ganinshi babu abunda yafi dadi irin karatun da zai koyawa dan adam ya fahimci yadda ubangiji Allah, ya tsara gan gar jikin mutun, da yadda jini yake gudu cikin jikin dan Adam, yadda sashe sashe na jikin dan adam yake aiki da kuma yadda cututtuka zasu iya kama jikin. Kana kuma irin maganin da za'a sha da yadda za'a sha maganin.

Amma na farko ga dukkan mai sha'awar karatun likita shine, yasa niyyar yin karatun dari bisa dari, karatu ne dake da yawan gaske, kuma yake bukatar mutum ya bada lokacin shi dari bisa dari. Idan mutum ya shiga karatun ba don yanada sha'awa ba, ko kuma baiyi niyyar bada lokacin shi dari bisa dari ba, toh za aga mutun yana samun matsaloli da dama. A ganin shi, karatun likita baya bukatar komai sama da dalibi mai sha'awar karatun da yake niyyar dagewa da bada hazaka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG