Kamfanin Sarafa Albasa a Nijar Zai Kawo Karshen Hasarar da Manomanta ke Yi

Mr.Morou Amadou, ministan shari'ar kasar Jamhuriyar Nijar

Za'a gina wani sabon kamfani da zai sarafa garin albasa a Jamhuriyar Nijar tare da saka hannun jarin 'yan kasuwa daga kasashen Burkina Faso da Ghana da Najeriya.

A Jamhuriyar Nijer yau aka yi bukin kaddamar da soma aiyukan kafa wata masana’antar sarrafa albasa a ci gaba da yunkurin tallafawa manoma samun hanyoyin sayerda anfanin noma da daraja.

A kalla million dubu 12 na sefa ne za a kashe domin aiyukan gina wannan masana’anta mai mazauni a garin Madawa na karkarar Tawa. Ana hasashen cewa masana’antar mai sunan SOTRACO SA za ta sayi tonne dubu 22 na albasa a kowace shekara daga hannun mazaunan karkaraALHAJI MUSTAPHA KADRI SARKIN ABZIN na daga cikinshugabanin kungiyoyin manoman albasa na kasar nijer .

Kimanin tonne dubu 5OO ne manoman albasake samarwa a kowace shekarasai dai su kan fuskanci matsaloli kafin su shigarda wannan anfanin nomazuwa ketaresaboda haka darektan bunkasa aiyukan noma na kasar Nijer ALHAJI ABDU UMANI ke ganin ta hanyar wannan sabuwar masana’antar sarrafa albasamatsalolin sun kusa zama tarihi .

Masu saka hannun jari daga kasashe kamar Burkina Faso Ghana da Najeriya da suka halarci wannan buki sun bayyana kyaukyawan fata a game da alfanun da aiyukan sarrafa albasar zai kawowa manoma da masu kasuwancin albasa ..

A daya bangaren kuma ta dalilin wannan masana’antar sarrafa albasadimbin matasan kasashen yankin Afirka ta yamma ne zasu sami aikin yi abinda zai kara taimakawa a yaki talauci da sauran miyagun aiyukan da zaman kashe wando ke jefa matasa ciki a yau.

Ga rahoton Souly Mummuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin Sarafa Albasa a Nijar Zai Kawo Karshen Hasarar da Manomanta ke Yi - 2' 37"