Kamfanin NNPC Ya Kulla Yarjejeniya Da Wasu Bankunan Waje

Tambarin kamfanin NNPC

Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya kulla wata yarjejeniya da wasu Bankuna na kasashen waje, da zata taimaka wajen inganta harkokin Man fetur da iskar Gas da kasar ke da su.

Shugaban kanfanin NNPC Injiniya Mai Kanti Baru, shine ya bayyana wannan yarjejeniyar a wajen wani taron kasa da kasa na Injiniyoyin hakar man fetur da aka gudanar a birnin Legas.

A cewar Mai Kanti Baru, wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen inganta hakko gangunan Man fetur Biliyan 37 da Najeriya ke da shi, da kuma iskar Gas kimanin Tiriliyan 199.

Kamar yadda wani masanin tattalin arziki da saka jari, Dakta Dauda Mohammad Kwantagora, ke cewa, wannan yarjejeniyar za ta taimaka wajen habbaka tattalin arzikin Najeriya, ta hanyar cin moriyar da masana’antun kasar zasu samu, wanda zai kai ga talakawa ta hanyar samar da ayyukan yi.

Cikin yarjejeniyoyin da aka samar kamar yadda shugabar kamfanin NNPC ya sanar, zasu taimaka wajen samar da makudan kudade tare da samar da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya.

Masana harkokin Man fetur na ganin wannan yarjeniyoyin da aka samar zasu taimaka wajen kawo karshen fasa bututun man fetur da ake yi a kasar, da kuma kawo karshen wahalar man fetur da ake a fadin kasar.

A kwanakin baya ma Najeriya ta rattaba hannu da kasar jamhuriyar Nijar na gina wata matatar man fetur a jihar Katsina, matatar da zata rika samun danyen man fetur daga kasar Nijar, da ake ganin hakan zai taimakawa kasashen biyu.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin NNPC Ya Kulla Yarjejeniya Da Wasu Bankuna - 4'45"