Alhaji Abubakar Sani Bello, gwamnan jihar Niger, ya musanta labarin cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
A wata hira da ya yi da Sashen Hausa a Minna bayan ya dawo daga tafiya ya ce ya yi matukar mamakin yadda aka yada labarin.
Yace zancen banza ne. Shi kansa bai ji maganar ba, sai daga baya wani ya fada masa. Ya ce yaushe za’a gina gida da shi ya zo ya bari. Da shi a PDP din yake kafin ya fita. Ya ce bashi da wani dalilin barin jam’iyyar APC.
Gwamnan yace yana cikin gwamnonin da suka dinga zagayawa suna yiwa ‘yan uwansu nasiha su ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar.
Gwamnan yace dukkan wadanda suka canja sheka basu fita don wata akida ba. Duk wadanda suka fita suna da wani dalilin yin hakan. Walau ko wani ya bata da mai gidanshi, ko yana gudun bincike ko kuma yana neman wani mukami.
Yin siyasa ba addini ba ne saboda haka mutum na da ‘yancin ya bar waccan jam’iyyar ya shiga wannan. Gwamnan ya kara da cewa yanzu aka fara siyasa. A tsaya aga abun da zai faru nan da wasu makonni masu zuwa.
Yace gwamnatin Shugaba Buhari ta yi bajinta wajen gudanar da ayyukan jin dadin jama’a cikinsu ko har da kammala babbar tashar jiragen ruwa dake Baro cikin jihar wadda y ace kwanannan za’a bude ta.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Facebook Forum