Kamfanin Huawei ya shirya fitar da sabbin kayayyakin fasaha da ya kera a kasuwar Najeriya, cikin kayayyakin kuwa harda sabon agogon sa TalkBand B2 da TalkBand N1, domin ‘yan Najeriya su sami cin moriyar fasahar.
Babban jami’i mai kula da harkokin cinikayya na kamfanin Huawei, Olaonipekun Okunowo ya bayyana cewa ‘karni mai zuwa na kamfanin zai ta’allaka ne kan wajen mayar da hankali kan kayayyakin tafi da gidan ka na wayoyin hannu.
Yakuma ce an shirya rubanya kasuwar kamfanin a Najeriya, agogunan kamfanin an kera sune domin biyan bukatun masu amfani da su. Babu shakka kan cewar agogunan hannu a wannan zamani sun zamo fasaha mai muhimmanci, ta hanyar cin moriyar ire iren wadannan fasahohi ne kamfanin Huawei ya shige gaba wajen jagorantar sauran kamfanoni don ganin an bunkasa a duniya, ita kanta Najeriya ba’a barta a baya ba.
Ya ci gaba da cewa, “zamu fara fitar da agogunan mu kasuwa a Najeriya, wanda zamu fara da agogon Talkband B2 a watan Augusta na wannan shekara.