Kamfanin Facebook Zai Kara Fadada Hanyar Zuba Labarai A Shafinsa

Facebook

Kwanan nan kamfanin shafin sada zumuncin FB zai kara fadada hanyoyin da masu amfani da shi za su sa labarai.

Nan ba da dadewa ba mutane za su iya nuna fushinsu, ko bacin rai, ko abin mamaki, ko kuma abinda ya burgesu, game da hoton ko bidiyon da wani ya sa a shafin.

Shugaban kamfanin na FB Mark Zuckerberg ya fada yau laraba cewa “Mu na son mutane su iya bayyana duk wasu muhimman abubuwa game da kansu, ba wai kawai abubuwan da su ka ji dadinsu ba ko wadanda mutane za su so in suka gani.

Kamfanin na FB ya fara gwada sabbin hanyoyin bayyana ra’ayoyin, a watan Oktobar shekarar da ta shige a kasar Chile, da Philippines, da Portugal da Ireland da Spain da Japan da kuma Colombia.

Kamfanin kuma na sa ran karin hanyoyin da mutum zai sa labarai zai karfafawa masu amfani da su guywa wajen bayyana ra’ayoyinsu akai-akai Su dinga kuma daukar dogon lokaci su na amfani da shafin fiye da yadda su ke yi yanzu.haka kuma kamfanin na shafin Fb ya sanar da cewa ya sami ribar dala miliyan daya da digo hamsin da shidda a watanni ukun karshen shekarar 2015, in aka danganta da na shekarar 2014 da ya sami ribar dala miliyan dari bakwai da daya.