Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Toyota Sun Kirkiri Sabuwar Motar Zamani Mai Tayoyi 3


Mota nai taya 3
Mota nai taya 3

Duniyar mottoci ta matso kusa, domin kuwa kamfanin mottoci na Toyota ya kirkiri wata mota da duk wani kamfani mai sana’ar kera motoci zai yi fahariya da kera irin wannan motar.

Tun baya ga wasu daga cikin kere-keren su na mutun-mutumi, sun kuma maida hankali wajen ganin sun samar da wasu irin motoci da zasu saukaka wahalar sufuri a kauyuka. Hakan yasa suka kera wannan motar mai tayoyi 3, an kuma samata suna “i-Road” wadda take idan tana kunne bakajin kukanta, kuma yadda take canza giyar ta ma babu wani alamar tanayi.

Irin kimiyar da aka saka a wajen kera wannan motar wadda take da banbanci da irin wadda akafi sani Keke Napep domin kuwa wannan anyi mata rufi da dai duk wasu abubuwa da motocin zamani suke da.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG