A ranar juma’a iyalan pasinjojin da suka gamu da ajalin su a hadduran jirgin saman Boeing 737 Max biyu, suka halarci zaman babban kotun kasa dake Texas, domin sauraren ba’asi, yayin da lauyoyin su suka nemi alkalin kotun yayi watsi da yarjejeniyar da ake son kullawa tsakanin masu kamfanin jirgin da masu gabatar da kara, cewa, a kyale kamfanin kawai ya fuskanci shari’a.
Lauyoyin nasu, sunyi kumfar bakin cewa, hukuncin da aka zartaswa kamafanin, da dududu na dala kimanin milyan 244 ne, yayi kadan, duba da alaifin karkatar da hankalin masu sa ido game da tsarin kula da na;urar tafiyar da jirgi da ya kai ga afkuwar hadduran. Sun zargi Boeing da ma’aikatar shari’a da laifin neman kauda ido daga gaskiya, da nuna halin ko in kula kan cewa, mutane 346 ne suka mutu a hadduran.
Wani alkalin Amurka na yanki Reed O’Connor, ya tambayi wani lauyan Boeing dalilin da yasa zai amince da wata tsararriyar yarjejeniyar sasantawa da wadanda ake karar.
Lauyan na Boeing, Ben Hatch yace Boeing wani jigo ne ga tattalin arziki da kuma tsaron kasa, da ke da bukatar sanin irin hukuncin da za’a yanke, kafin ya amince ya amsa laifin hadin bakin ga aikata damfara, da aikata wani babban laifi. Yace, domin kuwa ana iya haramtawa kamfanin samun kwangila daga tarayya.
Hatch ya kara da cewa, za’a jefa bangarori da yawa cikin shakku muddin aka gaza sanin irin hukuncin da za’a yanke, da suka hada da daukakin ma’aikatan kamfanin, da masu hannun jarin kamfanin, da daukakin masu alakar aiki da kamfanin daga cikin kasar da ma duniya baki daya.
Amsoshin dai sun harzuka yan’uwan wadanda hadurran suka rutsa da su.
Michael Stumo, wanda ya rasa diyar sa Samya a cikin hadarin na biyu, a bayan zaman kotun ya bayyana cewa, ‘kamfanin Boeing na ganin cewa yana da muhimmancin gaske ga tattalin arziki—sunfi karfin a daure su. Abinda yake fadi Kenan. An barsu su kashe mutane, ba tare da wani hukunci ba, saboda su manya ne, kuma masu hannun jari a kamfanin ba zasu so hakan ba.’
Itama gwamnati ta bi bayan Boeing din wajen neman alkalin ya amince da yarjejeniyar da aka cimmawa a watan Yuli.
Sean Tonolli, babban mataimakin shugaban sashen shari’a na bangaren laifuffukan damfara, yace, laifin hadin baki shine laifi mafi karfi da masu gabatar da kara zasu iya gabatarwa—ba yadda za’a yi su iya tabbatar da cewa, yaudarar da Boeing yayi ga bangaren nkula da tafiyar da jirgin ne ya haifar da hadurra, ya kuma ce, yin shari’a a kan hakan nada hadari.