Cikin wannan makon ne kamfanin Apple ya fitar da rahotan da ke nuna cinikin wayar kamfanin yayi ‘kasa, bai kai na shekarar da ta gabata ba.
Masu fashin baki dai sun yi hasashen cewa cikin wannan shekarar cinikin kamfanin zai ‘karu sosai, sai gashi hakan bai faru ba.
Duk kuwa da cewa Apple yayi kwantai a wannan shekarar, amma kuma ya samu kudi masu yawan gaske, kasancewar mutane sun sayi wayarsa mai tsada ta iphone 7 Plus. An dai sayar da wayar iphone akan farashin dalar Amurka $655 a wannan shekarar, a shekarar da ta gabata dai an sayar da ita kan farashin $642.
Kudin shiga da Apple ya samu ya ‘karu da kaso ‘daya cikin ‘dari inda ya kai Dala Biliyan 33.2 duk kuwa a dalilin wayar iphone 7 Plus. A cewar shugaban kamfanin Tim Cook, ba suyi hasashe mai kyau ba da suka zaci mutane zasu zabi waya mai girma jiki ba akan iphone 7.
Yawan wayar iphone da kamfanin ya taba sayarwa da ya shiga littafin tarihi itace Miliyan 78.3.
Your browser doesn’t support HTML5