KAMARU: Yan Aware Sun Yi Garkuwa Da Malaman Darikar Katolika Tare Da Kona Coci

Wani Mummunan Harin Cocin Katolika A Jihar Ondon Najeriya

Hukumomin kasar Kamaru sun zargi ‘yan aware da yin garkuwa da wasu limaman cocin Katolika guda biyar, da wasu masu ibada daga wata coci da ke kan iyakarta da Najeriya a yammacin kasar.

Cocin Katolika a Kamaru ta ce 'yan bindigar sun kona cocin, a garin Nchang ranar Juma'a kafin su gudu zuwa kan iyakar Najeriya.

Nchang ƙauye ne na yamma da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya.

Limaman na Kamaru sun ce sama da ‘yan bindiga 30 ne suka afka wa cocin a yammacin jiya Juma’a, inda suka yi ta harbe-harbe ta sama kafin su banka wa ginin cocin wuta. Sun ce an yi garkuwa da limaman coci guda biyar, da kuma masu ibada 3 akan babura zuwa daji da ke kan iyaka da Najeriya.

Aloysious Fondong Abangalo, limamin cocin na Mamfe inda Nchang yake, ya ziyarci cocin Saint Mary's . Ya ce harin da ‘yan awaren suka kai ranar Juma’a ya tsorata Kiristoci daga halartar cocin.

Abangalo ya ce ya yi mamakin yadda wasu mayakan da suka kai hari cocin Saint Mary’s tsoffin ‘yan cocin ne.

“Yan uwanmu ne suka aikata wannan abu, wasu daga cikinsu Kiristocin Katolika ne, abin kyama ne, kuna kona cocin, kuna gaya wa Allah ba ma son ka a kasarmu, wannan mummunan abu ne. Dukkanmu mu yi addu'a domin neman rahamar Ubangiji."