KAMARU: Kungiyar Doctors Without Border Na Nema A Dage Dakatar Da Ayyukanta

MSF DOCTORS WITHOUT BORDERS

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta agaji da ake kira Doctors Without Borders na kira ga hukumomin kasar Kamaru su hanzarta dage dakatar da ayyukanta na aikin likita a yankin Arewa maso Yammacin kasar Afirka ta Tsakiya.

Gwamnati ta haramta ayyukan kungiyar likitocin a watan Disambar da ya gabata. Bayan zargin kungiyar da tallafawa kungiyoyi masu dauke da makamai wadanda ba na gwamnati ba da ta saba bayyanawa a matsayin 'yan ta'adda. Kungiyar likitocin na Doctors Without Borders ta musanta zargin.

Doctors without borders

Tana kira ga gwamnati da ta fifita bukatun aikin jinya na dubun-dubatar 'yan ƙasa waɗanda ke buƙatar taimakon likita don rayuwa. Emmanuel Lampaert shine Mai Gudanar da Ayyuka na Kungiyar likitocin kasa da kasa ta agaji a Afirka ta Tsakiya.

Ya ce abin takaici ne yadda hukumomi za su dakatar da ayyukan jinya ga dubun-dubatar mutanen da ke bukatar kiwon lafiya. Lampaert ya fadawa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa manyan jami’an kungiyar sa zasu ci gaba da tattaunawa da hukumomi don dage takunkumin.