Kamaru  Da Aljeriya Sun Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Hadin Gwiwar Sojjojin Kasashen Biyu

Kamaru  Da Aljeria Sun Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Hada Sojjojin Kasashen Biyu

Ministan tsaron Kamaru ya ziyarci kasar Aljeriya tare da wata babbar tawagar sojoji, inda Joseph Beti Assomo ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Laftanar Janar Saïd Chenegriha.

YAOUNDÉ, CAMEROON - Kamaru da Aljeriya suna shirin wani gagarumin hadin gwiwa na sojjoji, idan muka yi la'akari da kalaman babban hafsan hafsoshin kasar Aljeriya, Saïd Chanegriha, wanda ya karbi baƙwancin Joseph Beti Assomo Ministan tsaron Jamhuriyar Kamaru a hedkwatar ma'aikatar tsaro da ke babban birnin Aljeriya.

‘Ya ce Ina da yaƙinin cewa dukkanmu muna da sha'awar yin aiki don kafawa da bunƙasa haɗin gwiwa mai ɗorewa, bisa dogaro, yin la'akari da moriyar juna da ƙarfafa tuntubar juna tsakanin cibiyoyinmu biyu”

A Kalamansa Janar Chanegriha ya sanar da cewar Aljeriya ta shirye gaba daya domin taimakeniya da Kamaru bisa gaskiya da adalci "a ɓangaren tsaro, da kuma musayar ƙwarewa a fannin inganta ƙarfin soja".

A nasa bangaren, Mista Joseph Beti Assomo ya yi maraba da wasiyyar da Aljeriya ta bayyana na ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa da Jamhuriyar Kamaru tare da sauran kasashen Afirka, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a ɗaukacin nahiyar ta Afirka.

Ƙasashen biyu na son a sanya wannan haɗin guiwa a tsakanin sojojinsu a cikin yarjejeniyar haɗin gwiwa ta soja, da za a amince da su a tsakanin bangarorin biyu, albarkacin ziyarar Minista Beti Assomo. Wadda za ta ba da damar bayyana abubuwan da za a iya cimma, ta kuma kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Wannan ziyarar dai za ta kasance share fage ga haɗin gwiwar soji da za ta daidaita manufofin shugabannin kasashen biyu .

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Aljeriya ya kammala da cewa, wannan ziyarar za ta zama shaida, ta yadda suka ƙuduri aniyar cimma muradun siyasar shugabannin kasashensu domin yin aiki tare, wajen aza harsashin haɗin gwiwa iri daban-daban, bisa la'akari, musanya ta gaskiya da tuntuɓar juna kamar yadda ya dace.

Wannan wata ziyara ce da take nuna ƙwazon da Aljeriya da Kamaru ke son sanyawa a cikin dangantakarsu, in ji Janar Saïd Shenegriha, wanda ya jaddada "bukatar haɗin gwiwa tsakanin sojojin biyu a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa ta soja don zaman aminci tsakanin bangarorin biyu”.

Saurari cikakken rahoton Mohamed Bashir Ladan:

Your browser doesn’t support HTML5

Kamaru  Da Aljeria Sun Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Hada Sojjojin Kasashen Biyu.mp3