Kamala Harris ta ziyarci wasu majami'u biyu a yankin Atlanta, inda ta yi kira ga bakaken fata a cikin majami'un da su fita su kada ƙuri'a.
A ranar 5 ga watan Nuwamba za a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka.
Fitaccen mawaki Stevie Wonder ya marawa Harris baya ya ja hankalin masu ibada a Jonesboro, Georgia, da wakar Bob Marley mai taken "Redemption Song."
Yada zango da Harris ta yi a majami'un wani bangare ne na wani shiri na kasa da aka sani da “souls to the polls.” Wannan wani yunkuri ne na karfafa mutane su fara zaben wuri a jihohin da za a fafata wajen neman kuri’u a zaben.
Bayan hidimar, motocin bas sun kai jama'ar kai-tsaye zuwa wuraren zabe don su yi sammakon kada kuri'aunsu.
Steven Wonder ne ya jagoranci jama'a a Jonesboro su rera wakarsa ta “Happy Birthday” ga mataimakiyar shugaban kasa wacce ta cika shekaru 60 a ranar Lahadi.