Kamala Harris ta gana da wasu mata 'yan kasuwa biyar daga fannonin daban-daban da suka hada da fannin magunguna da noma da yanayi da tattalin arziki da kuma al'adu. Hakan ya zo daidai da sanarwar alkawarin tallafin dalar Amurka biliyan 1 don taimakawa wajen cike gibin da ake samu tsakanin jinsi a fannin yanar gizo a nahiyar Afirka, da kuma taimakawa mata su kara shiga cikin harkokin tattalin arziki.
Ta ce, “Ina farin cikin sanar da ku a nan cewa Gidauniyar Bill da Melinda Gates, tare da gwamnatinmu za mu kafa Mata a cikin Tattalin Arziki na yanar gizo, da dala miliyan 60 daga asusun duniya, wanda za su magance damar ilimin harkokin yanar gizo da magance rashin daidaiton jinsi. Kuma gidauniyar Gate za ta zuba hannun jari na miliyan 40 domin tallafawa wannan burin.”
Kamala Harris ta kara da cewa, wasu kamfanoni masu zaman kansu sun yi alkawarin ba da na su tallafin wanda ke wakiltar sama da dalar Amurka biliyan daya, domin ci gaban mata a nahiyar Afirka, ta bangaren samarwa matan da ba a yi musu adalci ba, daidaiton a bangaren kiwon lafiya da kuma ilimi.
A hira da Muryar Amurka, ‘yar jarida Maryam Bawa ta yaba da wannan tallafi da ya fito daga kasar Amurka. Ta ce, zai yi matukar taimakawa a fannoni daban daban, musamman a ilimin kimiya da fasaha da yake an bar mata a baya.
Yayin da take Ghana, Kamala Harris ta ba da sanarwar bayar da tallafin dala biliyan 100 don taimakawa wajen magance barazanar ta'addanci da rashin zaman lafiya a kasashen Benin da Ghana da Guinea da Cote d'Ivoire da kuma Togo.
Domin Karin bayani ga rahotan Idriss Abdullah Bako:
Your browser doesn’t support HTML5