Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da matarsa Malama Zeenat Ibrahim El-Zakzaky da dansa Sayeed Aliy Ibrahim El-Zakzaki. Da kuma daya daga cikin manyan mataimakansa mai suna Sheikh Mahmud Turi wanda yake shugabantar ‘yan Shi’ar jihar Kano. Rikicin dai ya faro ne daga ranar Asabar da ta gabata sakamakon Muzaharar mabiya Shi’ar game da shirin yin mauludin su da suka saba duk shekara. Inda rahotannin suka nuna cewa sun tare hanyoyin wucewa a daidai lokacin da Babban Hafsan Sojojin Kasa Janar Tukur Buratai zai wuce.
A hanyarsa ta zuwa bikin yaye sojojin kasa na Najeriya a barikin Cindit Barrack da ke Zaria. Sojojin sun bayyana cewa ‘yan Shi’a sun tsare musu hanya a abin da suka zarga a matsayin yunkurin kai harin hallaka babban hafsan sojin. Su kuma ‘yan Shi’ar sun musanta wannan zargi. Shugaban mabiya Shi’a na jihar Katsina kuma daya daga cikin na hannun damar shi El-Zakzaky wato Malam Yakubu Yahaya Katsina ya bayyana mana a wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, sojojin sun dirar musu ne tare da rushe babbar cibiyarsu ta Bakiyyatul Husainiyya.
Daga baya kuma yin dirar mikiya a gidan shigaban nasu da ke Unguwar Gyellesu suka harbi na harba suka kama shugaban. Shi kansa El-Zakzaky kafin danke shi ya bayyanawa wakilinmu Isa Lawal Ikara cewa bas u yi yunkurin hallaka Buratai ba, sannan basu fito da makamai ba kamar yadda sojojin suka bayyana wa duniya. A bara dai an sami irin wannan arangama tsakaninsu da jami’an sojojin Najeriyar har aka kashe wasu ‘yan Shi’ar hade da kashe ‘ya’yan jagoran nasu na Najeriya har guda uku a artabun. Har ya zuwa lokacin buga labarin nan a shafinmu ba labarin inda aka nufa da Ibrahim El-Zakzaky. Ga yadda tattaunawarmu da Malam Yakubu Yahaya da kuma ta bakin kakakin rundunar sojan kasar Kanar Sani Usman Kukasheka.
Your browser doesn’t support HTML5