Kalubalen Da Na Fara Fuskanta A Harkar Waka Daga Iyaye -Inji Prince lazza

Prince lazza

Da farkon fara shiga ta harkar waka babban kalubalen da na fara fuskanta daga wajen iyaye na ne inda suka bukaci inyi karatu domin in samu aiki kamar na Banki ko wata ma’aikata maimamkon waka da na zaba wa kaina inji mawaki Abubakar Abdulaziz Prince lazz aka Mr levels.

Prince lazza, ya ce ya fara waka ne tun yana makarantar sakandire inda ya ke gayawa mutane abinda ke cikin zuciyarsa ta fagen waka, tare da samun wata natsuwa da isar da sako ga wadanda ya ke so su samu.

Prince Lazz, ya ce yana taba yanayin rayuwa na kunci, ko wata damuwa daga bangaren al’umma ta hanyar waka inda yake wake wannan matsala domin isar da sako.

Ya kara da cewa banda ma iyaye, abokai da ‘yan uwa duk basu mara masa baya ba domin ya cimma wani buri nasa.

Prince lazz, ya ce babban burinsa a yanzu ya canza tunanin mutane tare da fadakar da su cewar kowanne dan adam na da baiwar da Allah ya bashi tare da jan hankalin iyaye da su bar ‘ya’yansu wajen tabbatar da wata baiwa domin cimma muradansu.

Your browser doesn’t support HTML5

Kalubalen Da Na Fara Fuskanta A Harkar Waka Daga Iyaye -Inji Prince lazza