Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kelechi Iheanacho Ya Shiga Tarihi


Dan wasan gaba na kungiyar Super Eagles ta Najeriya mai taka Leda a kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, Kelechi Iheanacho, ya zamo dan wasa na farko da ya fara jefa kwallon da Mataimaki alkalin wasa na Bidiyo (VAR) ya tabbatar da cewa lallai kwallon ta shiga raga, wato ci ne, a gasar cin kofin kalu bale FA Cup na kasar Ingila,

Ita dai wannan fasaha ana amfani da ita ne wajan taimakawa alkalin wasa yayinda yake aikinsa ta wajan wani abu da ya faru da ake tantama wadda alkalin wasa bai gani ba, kama daga jefa kwallo a raga da ma sauransu, akan dawo da abun baya damin ganin gaskiyar lamarin kuma a yanke hukunci nan take.

Kelechi Iheanacho, ya samu shiga wannan tarihinne a wasan da kungiyarsa ta Leicester city ta doke takwararta ta Fleetwood town daci 2-0 a gasar FA Cup na bana. Ihenacho ya jefa duka kwallayen guda biyu ne a ragar Fleetwood, ya jefa kwallon farko a mintuna na 43 daga bisani ya sake zurara ta biyu a mintuna 77 haka dai aka tashi a wasan, inda kungiyar ta Leicester ta samu damar hayewa zuwa zagaye na gaba.

Wannan shine karo na uku da aka fara amfani da wannan fasaha ta (Vedio Assistance Referee) a wasannin kasar Ingila.

Anyi amfani da shi a wasan da aka buga tsakanin Brighton & Hove da Crystal palace a gasar ta FA Cup 2017/18 sai kuma Chelsea da Arsenal na kofin EFL 2017/18 Carabao Cup.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:25 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG