An shirya tsaf ana jiran zuwan al'amarin da ake yiwa kallon mafi mahimmanci a yakin neman zaben da zai share fagen zaben shugaban Amurka da zai gudana a ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Muhawarar da za'a fafata tsakanin mataimakiyar shugaban amurka 'yar jam'iyyar Democrat Kamala da abokin hamayyarta tsohon shugaban kasa Donald Trump a daren yau talata.
'Yan takarar 2 basu taba haduwa da juna ko yin magana ta wayar tarho ba, amma a yau Talata zasu tsaya daf da juna a Cibiyar Tsarin Mulkin Kasa dake birnin Philadelphia.
Sun shirya tsaf domin yin musayar yawu da juna tsawon mintuna 90 yayin da zasu rika amsa tambayoyin da masu karanta labarai a tashar talabijin ta ABC; David Muir da Linsey Davis za su rika jefa musu.
Dimbin milyoyin Amurkawa ne ake sa ran su kalli mahawarar da 'yan takarar shugabancin Amurka 2 zasu tafka a al'amarin daka iya zama mahawara daya tilo a yakin neman zaben.
Ku Duba Wannan Ma Miliyoyin Amurkawa Sun Shirya Tsaf Don Kallon Muhawarar Harris Da TrumpMahawarar na zuwa ne makonni 8 gabanin ranar zaben da gwamnati ta tsayar sai dai kwanaki kadan gabanin wa'adin da aka amincewa masu zabe da wuri su fara kada kuri'a a wasu daga cikin jihohin kasar 50.