KALLABI: Hira Da Linda Umaru PT2 Da Nazari Kan Tantance Asalin Masu Neman Aure, Janairu, 14, 2024

Alheri Grace Abdu

Shirin Kallabi na wannan makon ya kawo kashi na biyu na hira da Linda Umaru, wata 'yar arewacin Najeriya da ta fara sana'ar kitso a jihar California, wadda yanzu ta zama babbar 'yar kasuwa tana buga kirji da masu sana'ar 'yan kasar China.

A hirarta da shirin Kallabi, Linda ta yi tayin tallafawa duk macen da take da sha'awar fara sana'ar dinki a Najeriya idan aka tuntube ta.

Mun kuma yi dubi kan bukatar tantance asali da halayyar samari da 'yan mata kafin aure domin tabbatar da kafa zuri'a ta gari da kuma dorewar aure.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

Hira Da Linda Umaru PT2

Ku Duba Wannan Ma KALLABI: Hira Da Linda Umaru PT1 Da Nazari Kan Kalubalen Rayuwa A Najeriya