Da safiyar jiya Lahadi, a wani sakon Tweeter daga birnin Tokyo, Trump ya mai da martani ga kalaman John Bolton da ya yiwa manema labarai a baya, cewa ko shakka babu harba makami mai cin gajeren zango da Korea ta Arewa tayi ya sabawa kudurin Majalisar Dinkin Duniya.
Kalaman Bolton sune farko da jami’in na Amurka ya kwatanta gwajin makaman da Korea ta Arewa trayi a matsayin rashin mutunta kudurorin MDD.
Korea ta Arewa ta harba kananan makamai da mutane na da ma wasu mutane bassu ji dadi ba, amma banda ni, inji Trump yana fada a cikin wani sakon Tweeter sa.
Sakon Tweeter da Trump ya aike a kan batun Korea ta Arewa ya haifar da rikitarwa da al’ajabi, da ma acikin gwamnatinsa kadai ba, har ma kawayen Amurka na yankin, sun yi na’am da matsayar babban jamj’in fadar White House da yake bulaguro tare da shugaban kasar.
Wasu masu sharhi sun ce lallai harba makamai masu lizzamin abin damuwa ne.