Da yake ganawa da manema Labarai, Shanahan yace babu wani batun aika sojoji dubu biyar balle goma, inda yake bayani a kan rahoton kamfanin dillancin labaran Reuters cewa Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon tana niyar aika sojojin Amurka kimanin dubu biyar zuwa dubu goma Gabas ta Tsakiya.
Wannan bukatar kara dakarun yazo ne daga kommandan sojin ruwan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, Janar Kenneth Frank Mckenzie.
Shanahan yace wannan bukata ce da rundunar Amurka a Gabas Tsakiya ta CENTCOM ta saba neman karin sojoji amma kuma yace wannan wani batu ne da yakamata a bashi muhimmanci duba da al’amura dake faruwa a Gabas ta Tsakiya
Sai dai babu tabbas ko Fadar White House zata amince da aika wasu dakarun da jiragen ruwan yaki ba, da kuma kudaden da ake bukata.
Facebook Forum