Babban jami’in kare hakkokin bil’adama na Majalissar Dinkin Duniya mafi babban mukami, ya gargadi shugaban Amurka Donald Trump akan cewa caccakar da yake yiwa ‘yan jarida na iya sa wasu su nemi kaiwa ‘yan jaridar farmaki.
Trump ya sha sukar manyan kafafen yada labarai kamar su New York Times, da Washington Post, da CNN, ciki harda wanda yayi a farkon watan nan, a lokacin da ya caccaki kafafen yada labaran akan yadda suka bada rahoton mummunan gangamin da wasu turawa farar fata masu ra’ayin kyamar sauran jinsunan jama’a suka shirya a garin Charlottesville dake jihar Virginia, inda Trump ya kira ‘yan jaradar da lakabin “mugayen mutane marasa gaskiya”.
Akan haka ne, shugaban Hukumar kare hakkokin bil’adama na Majalissar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad Hussein ya fada yau Laraba a Geneva cewa, “kiran kafafen yada labarai da lakabin “masu bada labaran jabu” da shugaba Trump ke yi, yana matukar muzantasu.