Kalaman Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shatima Kan Addini Bai Dace Ba - Kungiyar Dattawan Arewa

Dr. Hakeem Baba Ahmed

Dr. Hakeem Baba Ahmed, ya zanta da wakilin Muryar Amurka jim kadan bayan wani taron manema labaru, inda ya ce 'yan-siyasa kan yi amfani da addini ne kawai lokacin neman kuru'u.

Kungiyar Dattawan Arewa ta ce kalaman Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shatima, kan addinan wadanda ya kamata a zaba a matsayin shugabannin majalissar kasa gobe Talata bai dace ba.

Mai-magana da yawun kungiyar, Dr. Hakeem Baba Ahmed, wanda ya zanta da wakilin Muryar Amurka a garin Kaduna jim kadan bayan wani taron manema labaru, ya ce 'yan-siyasa kan yi amfani da addini ne kawai lokacin neman kuru'u amma bayan cin zabe sai su yarda rigar addini su yi abun da su ka ga dama.

Saurari cikakkiyar hirar:

Your browser doesn’t support HTML5

Kalaman Mataimakin Shugaban Kasan Najeriya, Kashim Shatima Kan Addini Bai Dace Ba - Kungiyar Dattawan Arewa