Yan majalisar Najeriya masu jiran gado daga jam'iyya mai ci da na 'yan adawa sun hada kai wajen kafa wata kungiya mai suna JOINT TASK-10TH ASSEMBLY a turanci, wacce za ta tabbatar da goyon bayan duk wani shiri na shiya shiya da jamiyya mai mulki ta fitar domin zaben shugabanin majalisar.
Abuja, Nigeria —
Wanan kungiya ta ce ta kuduri aniyar yin taka tsantsan wajen sanin halayya, mutunci, cancantar yan takara a zaban shugabanin majalisar dokokin kasa ta 10 da kuma sauran manyan mukaman kaman yadda Shugaban kungiyar,Usman Kumo ya yi karin haske.
Kumo ya ce baya ga bin umurnin Jamiyyar APC a matsayin mai rinjaye a majalisar, muhimmin abu shi ne hadin kan Najeriya. Kumo ya ce kungiyar za ta kare mutuncin majalisar, tare da samar wa majalisar da cin gashin kanta, tabbatar da daidaito a yayin zaben shugabanin majalisar ta hanyar bin shawarar shiya shiya na jamiyyar APC mai mulki.
To saidai ga kwararre a fanin Siyasa da diflomasiyyar kasa da kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi nazari cewa
wannan Kungiya surkulle ne irin na yan siyasa da suka saba yi a Najeriya wanda a karshe za ta kare a neman mukamai da alfarma da ta ke ofisoshin da suke majalisa da kuma yadda Ofisoshin suke mu'amala da masu rike da harkar zartaswa,da irin kuma amfani da su a daidaikun su yan majalisa suke tunanin za su iya samu a wanna tafiya. Farouk ya ce suna tunanin lokacin raba damokradiyya ne ya zo, romon su ne za su fara rabawa, wane ne zai je ya hau babban kujera ya rika juyawa anai masa alfarma yana ci da gumin yan Najeriya.
Farouk ya ce yarda da suka yi da tsarin karba karba, ba abu ne zai haifar da hadin kai da za a ce duk shugaban da ya fito ta wannan tsari zai iya zama shugaban kowa, saboda haka tafiyar da mulkin sa zai dangana ne akan cewa alfarmar da aka yi masa daga shiyarsa ita ce abin da zai duba, sauran shiyoyin kuma ko oho.
Duk kokarin da Majalisa ta yi,akwai zubin da ake kiransu yan amshin shata domin ko a majalisa ta 9, an yi kungiya irin wannan wace ta ce za ta tabbatar komi ya tafi daidai na mutunta juna tsakanin majalisa da bangaren gwamnati
Amma ga dattijo kuma dan Majalisar Dattawa mai barin Ofis Sanata Adamu Bulkachuwa, ya tsokaci cewa .
Ba za a hana kowa fadin ra'ayinsa ba akan duk wani abu da majalisa ta yi, amma majalisa ta tara ta gaji majalisa ta takwas ne. Bulkachuwa ya ce Shugaban kasa ya samu matsala da majalisa ta takwas domin sun yi masa dabaibayi, ganin haka ya sa su a majalisa ta tara suka yi wa shugaban kasa sassauci saboda a samu tafiyar da mulki. Bulkachuwa ya ce a majalisa ta tara ma dai ba su zama yan amshin shata ba domin har sun yi wa shugaban kasa barazanar tsige shi bayan makonni 6 idan bai shawo kan tabarbarewar tsaro a kasar ba, kuma an ga sauyi a lokacin, saidai ba dayawa ba. Bulkachuwa ya ce Kungiya ta hadaka da yan adawa abu ne da ba zai dore ba, saboda idan sabon majalisa ta yi tutsu ba zai yi wa sabon shugaban kasa kyau ba.
Shi ma masanin harkokin zamantakewan dan adam kuma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum, Abubakar Aliyu Umar, ya ce ko da kungiya ko babu kungiya, yana ganin babu abinda zai sauya a Majalisar kasa
Abubakar ya ce wannan kungiya ba wani abu na sauyi ba ne, yaudara ce irin na yan majalisa. Abubakar ya ce suma sababbin za su zama yan anshin shata kamar na baya saboda duk abin da suke yi, suna yi ne domin muradun su
Kungiyar ta kunshi zababbun mambobin jamiyyar APC, da PDP,da Jamiyyar Leba da NNPP da APGA da SDP da ADC da Jamiyyar YPP wanda ya kawo jimlar zuwa jamiyyu takwas.
A saurari cikakken rahotun Medina Dauda: