Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Ba Zai Sake Tsayawa Takara Ba

Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, Paul Ryan

A wata sanarwar bazata kakakin Majalisar Dokokin Amurka ya ce bayan ya yi shekaru 20 a majalisa ba zai sake tsayawa takara ba, yanzu lokaci ya yi da zai koma gefe daya ya zauna da matarsa da 'ya'yansu uku

Kakakin majalisar wakilan Amurka Paul Ryan, ba zai yi takarar neman a sake zabensa a zaben da za'a yi cikin watan Nuwamban bana, wadda ya jawo ayar tambaya, ko jam'iyyar Republican zata ci gaba da zama mai rinjaye bayan zaben rabin wa'adin na bana?

A wani taro da manema labarai da yayi jiya Laraba, Ryan yace zai yi ritaya bayan wannan majalisa ta kammala aikinta a cikin watan Janairun badi.

Bayan shekaru 20 a majalisa, Ryan yace yana so ya samu lokaci sosai da uwargidansa da kuma 'yayansu uku.

Ritaya da kakakin majalisa Ryan zai yi, zai janyo zazzafar kamfen tsakanin 'yan jam'iyyar Republican kan wanda zai maye gurbinsa.