Kakakin Fadar White House Ya Kare Matsayin Shugaban Amurka Trump

Sean Spicer, Kakakin Fadar White House ta shugaba Trump

Fadar White House ta shugaban Amurka ta kare matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na korar mukaddashiyar Atoni Janar Sally Yates, saboda kin aiki ko kare dokar shugaban kasa, wacce ta takaita balaguro zuwa Amurka daga kasashe 7 da galibinsu musulmi ne.

Fadar ta kira matakin na Miss Yates "a zaman mai rudarwa da bijirewa umarni."

Miss Yates ta ki aiki da umarni wandayake kan doka, da aka yi da zummar kare Amurkawa," inji kakakin Fadar shugaban na Amurka Sean Spicer, lokacinda yake kare matakin na uban dakinsa jiya Talata a gaban manema labarai. Spicer ya kira matakin na Yates a zaman "cin amana" saboda haka yace "dai dai ne da aka cire ta daga kan mukaminta."

Haka nan Spicer, yayi kira ga 'yan Democrats a majalisar dattijai "su daina hana ruwa gudu da suke yi" su amince da zaben Jeff Sessions a zaman Atoni Janar, kuma su amince da sauran mutanen da shugaba Trump ya gabatar da sunayensu a zaman ministoci a gwamnatinsa.

Tunda farko a jiya Talata, Ministan Tsaron Cikin Gida John Kelly shima ya kare dokar ta shugaban kasa.

Yace "wannan ba dokar hana mutane zuwa Amurka bane, yace wannan dan tsaiko ne domin ya bamu damar mu sake nazarin shirin karbar 'yan gudun hijira da kuma hanyoyin da ake tantance su." inji Minista Kelly. Yace ba zamu yi wargi da rayukan Amurkawa ba,".

Duk da wannan dokar, jami'an gwamnatin ta Amurka suka ce za'a kyale 'yan gudun hijira 872 su dawo Amurka saboda matsanancin damuwa da suke ciki.