Ana harsashen cewa, ayyukan yada labaran kungiyar IS na tangal-tangal a kafofin sadarwa na internet, yayin da suke kokarin farfadowa, fiye da mako daya bayan da jami’an nahiyar Turai suka kai farmaki ga dubban shafukan su na aikewa da sakwannin.
Ba kamar yunkurin na baya na dakile kafofin farfagandar kungiyar ta ‘yan ta’adda ba, da ya samar da sakamako na wuccin gadi, jami’an yaki da ta’addanci da manazarta na cewa, matakin baya-bayan na da alamun yin tasiri mai dorewa.
“A iya sanin mu a yanzu, IS ba ta kan internet” a cewar Eric Van Der Sypt, mai magana da yawun ofishin babban mai gabatar da kara na kasar Belgium, a wani taron manema labarai makon da ya gabata a birnin Hague.
Ya zuwa yanzu kadai, sakamakon ayyukan da ‘yan sandan hadin gwiwar Turai, da kungiyar tarayyar turai su ke yi da kamfanonin samar da kafofin internet kamar Telegram, Twitter, Google da Instagram, ya tabbatar da wannan kiyasin.