Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Gudanar Da Taron Tattaunawa Akan Sauyin Yanayi


Wakilai daga kasashe kusan dari biyu a yau Litinin, sun soma zaman tattaunawa akan yanayi a birnin Madrid, sakamakon fargaban ganin alamun mummunan gurbatar yanayi, da kuma ficewar Amurka daga taron kawancen yaki da shi a duniya.

Wasu tagwayen rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da ta wallafa a ‘yan kwanakin nan sun bayyana illolin da rashin daukar isassun matakan kare yanayi suke haifarwa, da kuma yadda suke shafar rayuwar al’umma, musamman sakamakon zanga-zangar da ake ta yi a fadin duniya a ranar Juma’a, da ke nuna karfin jama’a.

Taron wanda ke karkashin shugabancin kasar Chile da ta janye daga karbar bakuncin sa sakamakon rikicin cikin gida, da aka yi wa lakabi da COP 25, na da burin cimma matsaya a kan dokokin aiwatar da shawarwarin da aka cimma na yanayi a taron Paris na shekara ta 2015.

Masana sha’anin muhallin na fatan taron zai samar da tubali ga kasashe, su kara azama wajen shuke-shuken itatuwa da rage amfani da iskar gas kafin taron shekarar badi da za’a gudanar a birnin Glasgow na kasar Scotland.

Kwana daya kafin taron na birnin Madrid, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana kokarin da kasashen duniya ke yi na yaki da sauyin yanayi da cewa ko kadan bai isa ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG