Kafofin Sada Zumunta Na Taka Rawa Wajen Tabarbarewar Tarbiyya A Yankin Arewancin Najeriya - Masana

kafofin sada zumunta

La’akari da irin  rawar da kafofin sada zumunta ke takawa a rayuwar al’umma, kwararru na ganin ya kamata a dauki matakai wajen magance matsalolin da kan kunno kai saboda irin abubuwan da wasu da suka yi fice ke wallafawa a kafofin sada zumunta, da ke yin tasiri wajen gyara ko bata tarbiyar al’umma.

Daya daga cikin manyan abubuwan da ke tasiri a rayuwar bil'adama shi ne amfani da kafafen sada zumunta, inda miliyoyin al'ummar duniya ke mu’amala da su. Yayin da wasu ke shiga don sada zumunci wasu kuwa dan suyi suna ne ko su nemi kudi.

A arewacin Najeriya wasu da yawa sun yi fice ta hanyar samun mabiya masu yawa a kafofin sada zumunta, amma yadda suke amfani da kafofin abin damuwa da takaici ne matuka, musamman yadda ake zargin suna zubar da kimar addini da al’ada.

Kwararru a fannin fasaha na ganin bin doka da kuma amfani da kafofin sada zumunta yadda ya kamata abu ne mai matukar wahala.

Yusuf A Yusuf ya ce da za a yi ayyukan Allah ba wani abu na lalata tarbiya ba, to ba lallai ne fitattun nan su samu magoya bayan da suka tara ba, balle har su samu kudin shiga.

Dr. Na’ima Idris, matashiya ce da tayi fice a kafofin sada zumunta, ta shaida wa Muryar Amurka cewa ba duka aka taru aka zama daya ba.

To sai dai ana ganin iyaye zasu taka rawar gani wajen kiyaye tarbiyar ‘ya'yansu, kamar yadda Hajiya Asmau Umar Mairiga ta fadi.

Kafar sada zumunta makaranta ce ta kanta, domin ko ba komai ta nan ne wasu ke bibiyar fitattatu don su kwaikwayi yadda suke tafiyar da al’amuransu na yau da kullum. Sai dai kuma yadda hakan ke tasiri a rayuwar mutane abin dubawa ne.

Saurari rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

Kafofin Sada Zumunta Na Taka Rawa Wajen Tabarbarewar Tarbiyya A Yankin Arewancin Najeriya - Masana