Yanzu haka dai masana dokoki na ganin lokaci yayi da Majalisar dokokin Najeriya za ta samar da doka ta musamman akan ta’ammali da kafofin sadarwa na sada zumunci.
A ranar litinin da ta gabata ne kotun majistiren Kano dake Noman’s land karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Gabari ta samu Mubarak Muhammad Bala da Naziru Muhammad da laifin amfani da kafar Tiktok kuma suka aikata laifi, al’amarin da ya sanya yanke musu hukuncin bulala 20 kowane da tarar naira dubu 10, kana kuma da sharar harabar kotun tsawon kwanakin 30.
A tattaunawa da wasu daga cikin ‘yan Najeriya a Kano, sun fadawa Muryar Amurka cewa, hukuncin yayi dai-dai, suna masu cewa, hakan ka iya zama darasi ga sauran matasa masu tunani irin wannan.
Dr Musa Abdullahi Sufi na cikin wadanda suka yi shuhura wajen rubuce-rubuce a kafar sada zumunci ta zamani wadanda ake kira social media Influencers.
Ya yi karin bayani kan kokarin su na jan hankalin matasa game da amfani da wannan kafa ta hanyar da ta dace. “ A duk lokacin da naga wani yayi rubutu ko tsokacin da bai kamata ba, na kan kira shi a waya in ja hankalinsa kan rashin dacewa ko hadarin da ke tattare da abinda ya rubuta ko kuma ya saka a shafin san na sada zumunta . Kafin haka ni a karan kaina ni kan tsaya in tace in yi nazari sosai akan martani ko amsoshin da zan rubuta a duk lokacin da ake mahawara akan wannan batu”
Tuni dai ma’abuta shari’a da dokokin kasa ke ganin cewa, lokacin yayi da majalisar dokokin Najeriya ya kamata ta samar da wata doka ta musamman kan amfani da kafar sada zumunci ta zamani, la’akari da yadda ‘yan kasar suka rungume ta, musamman matasa.
A nata bayanin, Barr Amina Umar Hussain ta kungiyar lauyoyi mata a Najeriya, tace dukan dokokin da ake amfani dasu wajen yanke hukunci akan ire-iren wadannan batutuwa za’a iya cewa sun tsufa, don haka kamata yayi ‘yan majalisar dokoki su yi hobbasa wajen samar da sabbin dokoki da za su dace da yanayin da ake ciki a yanzu.