A yayin taron laccar da aka gudanar a harabar kwalejin ta Excel, an kalubalanci musulmi su rinka nuna halaye na gari abin koyi a kalaman su da ayyukan su da kuma mu’amalar su ta yau da kullum, domin kawar da gurguwar fahimtar da ma’abuta wasu addinai a sassan duniya ke yiwa musulinci.
Ustaz Abdullahi Musa Pen Abdul wanda ya gabatar da makala a wurin laccar yace akwai bukatar a fahimci me ake nufi da musulinci, ka’idojinsa da sharruda, kana a gane wanene musulmi.
Farfesa Nura Muhammad Sani mataimakin shugaban Jami’ar tarayya dake Dutse a Jihar Jigawa yace la’akari da cewa, baya ga koyar da ilimi, alhakin tarbiyyar dalibai ya rataya a wuya malamai, ya sanya hukumar gudanarwa ta Jami’ar hadin gwiwa da kungiyoyin dalibai kan shirya tarukan lacca akan al’amuran addini dana yau da kullum.
Sai dai Ustaz Abdullahi Musa yace akwai bukatar musulmi ma’abuta kafar sada zumunta ta zamani su fahimtar da duniya hakikanin musulinci a aikace ta hanyar baje kolin su a wadannan kafofi domin isar da sakonni ga jama’a.
A hirar shi da Muryar Amurka, daya daga cikin masu fada a ji a kafar sada zumunta, Dr Musa Abdullahi Sufi, yace yanzu haka an samar da wani zaure da aka yiwa lakabi da Dandalin masu fada a ji a shafukan sada zumunta, 'yan arewacin Najeriya da nufin samar da alkibila guda akan al’amuran da suka shafi arewa, musamman ta fuskar zamantakewa, addini, da tattalin arziki.
Kamar sauran sassan duniya, miliyoyin ‘yan Najeriya ne ke amfani da kafofin sada zumunta na whatsApp, da facebook, da twitter, da tiktok da sauran su wajen karba ko isar da sakonni a dare da rana.
Saurari rahoton cikin sauti: