Mai horar da ‘yan wasan kasar Egypt Carlos Quieroz ya yi korafin cewa kafafen yada labaran kasar ba sa yi wa ‘yan wasan kasar adalci.
A cewar Quieroz, kafafen yada labaran kasar ta Egypt suna yawan sukarsu tun da aka fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a Kamaru.
A ranar Laraba ‘yan wasan na Pharoah suka cire Ivory Coast da bugun fenariti da ci 5-4 bayan da aka tashi a wasan babu wanda ya ci kwallo ko daya cikin mintina 120.
“’Yan wasan sun cancanci su kai zagaye na gaba, ina ga ya kamata a nuna musu girmamawa, tausayi da tare da nuna musu hakuri, musamman daga masu sharhi da kafafen yada labaran cikin gida, sun jima suna ta caccakar tawagar da ‘yan wasanta.” Quieroz ya ce.
Dan wasan Liverpool Mo Salah ne ya buga fenaritin karshe da ta ba Egypt nasarar shiga zagayen quarter-finals
Quieroz ya yi amfani da taron manema labarai da ake yi bayan kammala wasa, ya bayyana korafin nasa.
Egypt za ta kara da Morocco a zagayen na quarter-finals a ranar Lahadi.
A daya wasan da aka yi kuma, Equatorial-Guinea ita ma ta doke Mali da bugun fenariti.
Za ta hadu da Senegal a wasan quarter-finals a ranar Lahadi.